Monday, 12 November 2018

An yiwa shugaba Buhari da Ganduje addu'a a Kano

Dan amajalisar wakilai me wakiltar Kiru da Bebeji daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa sun gudanar da addu'o'i da suka saba yi lokaci zuwa lokaci a mazabar tashi inda suka wa Najeriya addu'ar zaman lafiya,hadin kai da ci gaba.Ya kara da cewa sun wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje addu'a, ya kara da cewa shahararren alarammannan, Ahmad Sulaiman ya halarci gurin addu'ar.

Muna fatan Allah ya amsa.


No comments:

Post a Comment