Tuesday, 6 November 2018

Ana gasar shiga kasuwar Kaduna tsakanin Gwamna El-Rufai da Sanata Shehu Sani

A kwanakin bayane yayin da tsama tayi tsauri tsakanin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, gwamnan ya kalubalanci Sanata Shehu Sani da cewa bashi da karbuwa a gurin jama'ar Kaduna idan kuma yana ja to su shiga babbar kasuwar Kaduna aga wanda zai fito lafiya.


Tun a wancan lokacin sanata Shehu Sani ya shiga kasuwar Sheikh Gumi babu jami'an tsaro inda ya gaggaisa da 'yan kasuwa ya kuma kalubalanci gwamnan da shima ya shigo kasuwar babu jami'an tsaro.

Haka kuma jiya, Sanata Shehu Sani ya sake shiga kasuwar inda ya saka hoton bidiyon yanda  'yan kasuwan suka mai kyakkyawar tarba.

To a yau shima, Gwamna El-Rufai ya shiga kasuwar inda har ya gana da masu sayarwa, gyara da kuma saida kayan amfanin wayoyin hannu, gwamnan ya musu alkawarin cewa zai sama musu yana yi me kyau da kuma basu horaswa yanda zasu inganta sana'ar tasu.


No comments:

Post a Comment