Saturday, 10 November 2018

APC Ba Ta Da Dantakar Gwamna A Jihar Zamfara

A jiya Juma’a ce Hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar da sunayen ‘yan takarar majalisar jiha da kuma na gwamna a jihar Zamfara amma daga cikin sunayen da Hukumar ta fitar babu sunan wani dantakara daga jam’iyyar APC.

Majiyarmu ta shaida mana cewa Hukumar ta kafe sunayen ‘yan takara ne a ofishinta da ke Gusau a jiya Juma’a.

Jam’iyyu da sunayen ‘yan takararsu ke ciki  su ne: APGA, PDP, NRM, SDP, PRP, GPN da kuma NCP.

Da take Magana da manema labarai jim kadan bayan mannan sunayen kwamishinar Hukumar mai kula da Sakkwato da Kebbi da Zamfara Hajiya Amina Zakari tace a cikin sunayen da aka aiko musu ba ‘yan takara daga jam’iyyar APC
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment