Saturday, 10 November 2018

Arsenal ta yi wasanni 15 ba tare da shan kaye ba

Arsenal ta samu nasarar kaiwa zagaye na gaba, wato siri daya kwale mai dauke da kungiyoyi 32, duk da cewa ta tashi canjaras ne wato babu ci 0-0, a wasan gasar Europa da ta fafata da Sporting Lisbon a ranar Alhamis.


Yayin wasan na rukunin 5 da Arsenal ke ciki, kungiyar Vorskla Poltava ta Ukraine ta yi rashin nasara har gida a hannun Qarabag daga Azerbaijan, abinda ya karfafa nasarar kaiwa mataki na gaba da Arsenal din ta yi.

Sai dai yayin wasan na gasar Europa, dan wasan gaba na Arsenal Danny Welbeck ya samu rauni, wanda ake fargabar zai iya tilasta masa shafe lokaci mai tsawo yana jinya.

Wasan na ranar Alhamis ya kara yawan wasannin da kungiyar ta Arsenal ta fafata ba tare da shan kaye ba, inda a yanzu ta samu nasara a jimillar wasanni 15 a jere.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment