Tuesday, 27 November 2018

Babu tantama nine zan sake cin zabe a Kaduna>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tabbatar da cewa, alamun da yake gani kamar ya sake lashe zabe ya gamane, gwamnan ya bayyana hakane a taron kwamitin habaka harkar kudi da tattalin arziki na kasa da ya wakana a Kaduna.


Gwamnan ya kara da cewa, sake cin zabe bashine abu mafi muhimmanci ba amma yin abinda ya dace ta yanda wanda zasu zo nan gaba zasu yaba.

Saidai ya ce; daga alamun da yake gani duk da mutanen da ake cewa sun batawa rai amma zaben shekara me zuwa shine zai lasheshi, kamar yanda Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment