Tuesday, 27 November 2018

Bacci ya dauke direban jirgin sama yana tuki

Hukumomin da ke kula da lafiyar jirage sun ce wani karamin jirgi da ya kamata ya sauka a Australia ya wuce da gudu bayan direban jirgin ya yi bacci.


Direben jirgin kadai ne wanda ya ke cikin jirgin da ya tashi daga Devonport zuwa King Island zuwa Tasmania a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Hukumar da ke kula da harkokin jiragen sama ta Australia ATSB na gudanar bincike kan al'amarin.

Har yanzu hukumomi ba su bayyana yadda direban jirgin ya sauka daga cikinsa lami lafiya ba.

A shafinsu na intanet, Vortex Air sun ce aikinsu ya shafi daukar shatar jirgin sama ga kungiyoyi da kamfanoni da masu yawon shakatawa a Australia.

Hukumar ATSB sun ce za su tattauna da direban jirgin kuma za su binciki yadda ake tafiyar da jirgin kafin a fitar da rahoton zuwa badi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment