Tuesday, 27 November 2018

Ban baiwa EFCC da ICPC tallafin miliyan 10 ba>>Gwamna Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta fito ta karyata labarin dake cewa, wai gwamnan jihar ya bayar da kyautar naira miliyan 10 ga hukimomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC.


Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a sanarwar farko da gwamnatin jihar ta fitar tace ta bayar da tallafin naira miliyan 10 ga hukumonin EFCC, ICPC, da AFN wanda sune suka shirya wani gangamin motsa jiki.

Saidai a wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar yau tace hukumar, Fair Play Sports International Agency wadda me zaman kantace kuma itace ta shirya wannan gangami na motsa jiki ta baiwa kyautar miliyan 10.

Ta kara da cewa anwa sanarwar farko fassarar ba daidai ba, gwamnatin kano bata bayarba kuma bata da niyyar bayar da tallafin kudi ga hukumomin EFCC da ICPC.

No comments:

Post a Comment