Friday, 2 November 2018

Ban karbi daloliba batamin sunane kawai aka shirya yi>>Gwamna Ganduje

Gwammnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kauracewa kwamitin binciken da majalisar jihar Kano ta kafa kan bidiyon zargin karbar rashawa daga 'yan kwangila, inda ya tura kwamishina watsa labarai na jihar Malam Muhammadu Garba ya wakilce shi.


Majalisar ta gayyaci gwamna ganduje domin ji daga bakinsa kan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, inda a ciki aka nuna 'gwamnan' yana karbar bandir-bandir na dalar Amurka daga wajen 'yan kwangila.

Tun da safiyar Juma'ar nan ne, 'yan jarida da kungiyoyin al'umma da kuma 'yan kallo suka hallara a harabar majalisar, ana dakon zuwan gwamnan.

To sai dai kwamishin watsa labarai Malam Muhammad Garba wanda ya wakilci gwamnan yace, gwamnan yana da zabi ya je da kansa ko kuma ya tura wakilci.

Ya kara da cewa Ganduje ya tura wakilci ne saboda girmama majalisar.

A jawabansa dangane da bidiyon, Malam Muhammad Garba ya musanta cewa bidiyon suna da inganci, ya ce an shirya su ne kawai domin a batawa gwamnan Kano suna, da kuma makarkashiyar siyasa, musamman yanzu da ake tunkarar zabukan 2019.

A makon da ya gabata dai dan jaridar da ya wallafa bidiyon ya bayyana a gaban kwamitin inda ya jadda cewa, bidiyon sahihai ne, sai dai bai bayyana daga inda ya same su ba.

Kwamitin na majalisar dokokin Kano da ke bincike kan zarge-zargen bai yi wa kwamishin tambayoyi ba, saboda a cewarsa ba kwamishina ake zargi ba, Gwamna Ganduje ake zargi, don haka shi ne kadai zai iya amsa tambaoyin da suke da su.

Kwamitin wanda ke karkashin Baffa Babba Danagudi ya ce zai je ya yi nazarin bidiyon, sannan zai cimma matsaya kan batun zuwa ranar Talata mai zuwa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment