Tuesday, 6 November 2018

Ban yi aure ba>>Rashida Lobbo

Jarumar fina-finan Hausa, Rashida Lobbo ta fito ta warware zare da abawa akan wata magana da ake yadawa akanta a shafukan sada zumunta na yanar gizo cewa wai ta yi aure.


Rashida tace taje wajan 'yan uwanta a kasar Kamaru kuma an mata baiko amma maganar gaskiya itace ba'a daura mata aure ba.

Ta kara da cewa tana godiya da fatan Alheri da mutane su kai ta mata kuma auren nata ma nan ba da dadewa ba za'a yishi.

No comments:

Post a Comment