Saturday, 10 November 2018

Bayan dan Obasanjo an sake samun dan wani babban dan PDP da ya bijire mai yace shima Buhari zaiwa Kamfe

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma Olusegun Obasanjo, Dr. Doyin Okupe, ya bayyana karara cewa yaronsa, Ditan, ya zabi yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin zabe kawai don ya kuntata masa, saboda sabanin da ke a tsakaninsu.

Okupe, wanda ya taya dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Dr. Bukola Saraki yakin zabe a lokacin zabukan fitar da gwani, ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter, bayan yaci karo da wasu hotuna da kakakin kungiyar yakin zaben Buhari 2019 ya wallafa, na cewar yaron nasa na dawo tafiyar suugaban kasar.

Dr. Doyin Okupe, ya ce: "Ditan yarona ne. Yana da ilimi sosai, musamman duba da manyan makarantun da ya halarta wajen yin ilimin lauyanci. Sai dai mun dade muna samun sabani a cikin shekaru 5 dinnan. Watakil, wannan ne dalilinsa na bin Buhari don ya cusa mun bakin ciki. Duk da hakan ina masa fatan alkairi."
Ko da ma'abota amfani da shafin na Twitter suka matsa masa lamba kan cikakken bayanin abubuwa da ke faruwa tsakaninsa da yaron nasa, Mr. Okupe ya bayyana cewa, "Zai zama abu mai matukar wahala fahimar da jama'a matsalolin iyali, don haka mu kaucewa shiga lamuran da basu shafemu kai tsaye ba."

"Ba zan taba tona matsalar da ke tsakani na da Ditan ba kuma ba zan taba bayyana hakan ga jama'a ba, ko da kuwa hakan zai jawo babbar asara ga siyasata. Ina sonsa har cikin zuciyata.

"Na samu labarin yadda yake kokarin samun ganawa da abokan hamayyar siyasata kamarsu Tinubu, Kashamu, OGD da sauransu, don hada kai da su. To ni a wajena, kuma a wajensa, wannan ne lokacinsa. Wannan siyasa ce kawai, wacce kuma ni gwani ne. Yoruba na cewa, ba wai ranar da yaro ya la'anci bishiyar Iroko ba ne bishiyar take fadawa akansa ba, a'a, takan jira har washe gari."
Legit.ng

No comments:

Post a Comment