Tuesday, 27 November 2018

Bayan Talauci, Nijeriya Na Gab Da Zarce Indiya A Yawan Masu Bahaya A Sararin Allah

A kasashen duniya Nijeriya ce kasa ta biyu wadda take bin kasar Indiya idan ana maganar yin Bahaya a fili, ta kuma kasance ta daya a nahiyar Afirka. 

A cikin wannan shekarar da muke ne dai aka samu rahotannin da suka bayyana cewa, Nijeriyar ta zarta kasar Indiya da yawan matalauta inda yanzu ta zama ta daya a Duniya.

Wani mizani wanda ake gwada halin da kasa take ciki dangane da rahoton (MICS) na shekarar 2017, wanda ya bayyana cewar kashi 28.5 na al’ummar Nijeriya suna yin Bahaya a fili,  ya yin da kuma wasu milyan 110  basu da hanyar da zasu inganta al’amarin tsaftace muhalli. 

Gaba daya dai masana sun bayyana cewar Nijeriya ya kamata tayi duk abubuwan da suka kamata ba wai yawan magana ba, akan al’amuran da suka shafi tsaftace muhalli da kuma tsaftataccen ruwan sha, sun kuma yi kira ga ayi tsare tsare da kuma manufofi wadanda zasu kawo canji akan yadda mutane zasu gyara halayensu akan al’amarin daya shafi tsaftace muhalli.
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment