Wednesday, 28 November 2018

Bidiyo ba zai hanani cin zabeba>>Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce yada bidiyon da ake yi na zarginsa yana karbar kudin rashawa daga 'yan kwangila ba zai hana shi cin zabe ba a 2019.


Ganduje ya ce wasu 'yan hamayya sun dogara wajen yada bidiyon zargin karbar kudaden a matsayin hanyar da za ta kai su ga cin zabe.

Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da yake magana da wasu 'yan kasuwa a fadar gwamnatin Kano.

Wannan ne karon farko da Ganduje ya yi magana a fili kan batun bidiyoyin da ake yadawa na zargin karbar kudade daga 'yan kwangila.

"Suna nan suna jira za su ci zabe a bidiyo," a cewar Ganduje a lokacin da ake yi masa sowa da tafi.

Ya yi zargin cewa bokan masu hamayya da shi ne ya fada musu cewa za su yi nasara a zaben, tun da akwai bidiyon zargin karbar cin hanci.

To sai dai a yayin jawabin, Ganduje bai ambaci sunan wasu mutane da yake zargi suna amfani da bidiyon domin cimma manufar siyasa ba. To amma akwai zazzafar hamayyar siyasa tsakaninsa da 'yan PDP musamman bangaren tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwamkwaso.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment