Thursday, 29 November 2018

Boko Haram 'na kai wa sojoji hari da jirage marasa matuka'

Rundunar sojan Najeriya ta ce kungiyar Boko Haram ta fara amfani da jirage marasa matuka domin kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin kasar.

Haka kuma rundunar ta ce ta lura cewa wasu mayaka daga kasashen waje na shiga Najeriya domin taimakawa kungiyar ta Boko haram a farmakin da take kai wa dakarun tsaron Najeriya.

Wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar a madadin hafsan hafsoshin sojan kasa Laftanal Tukur Burutai ta ce kungiyar ta fara amfani da jiragen ne da kuma mayakan waje cikin watanni biyu zuwa uku da suka gabata.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sojoji 23 ne aka kashe a harin da 'yan Boko Haram din suka kai Metele ranar 18 ga watan nan na Nuwamba, sannan wasu 31 kuma suka jikkata.

Rundunar sojan ta Najeriya ta ce ala tilas sojojin suka ja da baya sannan aka yi wa bataliyarsu mummuna ta'adi.

Wannan ne dai karon farko da rundunar sojan Najeriya ta bayyana yawan sojojin da aka kashe a harin na Metele, bayan wasu bayanai da ba na hukuma ba sun nuna muni da girman harin.

Wasu kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewa sojojin da aka kashe sun haura 100 a harin na Metele.

Janar Kukasheka ya kara da cewa a 'yan makwannin nan kungiyar ta Boko Haram ta zafafa kai hare-hare a kan sojojin Najeriya a arewa maso gabashin kasar.

"A duka hare-haren sojojin mu sun yi nasarar dakile su tare da kashe mayakan na Boko Haram da dama. Sai dai an kashe sojoji 16, yayin da 12 kuma suka jikkata," in ji Kukasheka.

Wuraren da aka fi kai hare-haren kan dakarun Najeriya sun hada da Kukawa da Ngoshe, da Kareto da Gajiram.

Sanarwar na zuwa ne a ranar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno bayan hare-haren, inda kuma ya duba wasu daga cikin sojojin da suka jikkata.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya ce ya kira wani taron da shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi domin tattaunawa kan batun na Boko Haram.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment