Wednesday, 28 November 2018

Buhari Ya Ba Rundunar Soja Umarnin Murkushe Mayakan Boko Haram

Shugaba Muhammad Buhari ya ba rundunar Sojan Nijeriya Umarnin kawo karshen duk wata barazana na mayakan Boko Haram inda ya jaddada cewa dole a yi nasara a yakin da ake yi da 'yan ta'addan.


Buhari ya bayar da wannan umarnin ne a yau Laraba a lokacin da ya halarci taron shekara shekara na rundunar Sojan kasa da aka gudanar a Maiduguri inda ya shawarci sojoji kan kada su bari a dauke masu hankali a yunkurin da suke yi na kawo karshen ta'addancin Boko Haram sannan kuma ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta samar masu kayan yaki na zamani.
Rariya.

No comments:

Post a Comment