Tuesday, 6 November 2018

Buhari Ya Karbi Rahoton Mafi Karancin Albashi Na 30,000

Shugaba Muhammad Buhari ya karbi rahoton mafi karancin albashi na Naira 30,000 wanda aka cimma yarjejeniya da kungiyar Kwadago a daren jiya Litinin inda ya jaddada cewa ma'aikata sun cancanci wannan karin albashi musamman yadda farashin kayayyaki suka tsawwala.


Buhari ya bayar da tabbacin daukar matakan da suka dace wajen gabatar d kudirin karin albashin ga majalisar tarayya don amincewarsu ta yadda zai zama doka inda ya nemi a yi hakuri da gwamnatinsa na 'yan makonni masu zuwa a yunkurin ganin an samu aiwatar da sabon tsarin albashin.
Rariya.

No comments:

Post a Comment