Saturday, 10 November 2018

Buharine zabine inji Ali Nuhu

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu a karin farko ya saka hoton shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya bayana cewa shine shugaban kasarshi, Ali Nuhu dai a da be bayyana matsayarshi ba amma yanzu ya fito ya nuna yana tare da shugaba Buhari.


Koda a jiya, Juma'a Ali yana cikin tawagar da suka kaiwa matar shugaban kasa, A'isha Buhari ziyara a Villa inda har ta basu kyautukan karramawa.

No comments:

Post a Comment