Tuesday, 27 November 2018

Bukatar A Dauke Shari'ar Janar Alkali Daga Jihar Filato

Ni Alhaji Nura Abubakar Waziri wanda aka fi sani da Magayakin Shugaba Buhari, ina kira da babbar murya ina kuma jan hakalin ministin shari'a Abubakar Malami, sannan alkalin alkalai na kasa baki daya, Mai Shari'a Onogeb, da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad na uku, da Shiek Khalid Sakatren JNI da kuma Shiek Abdullahi Bala Lau, daga karshe Shiek Sani Yahya Jingir da dukan girmamawa akan shari'a da ake yi ma kabilar Birom da suka kashe Janar Alkali da a dauke wanan shari'a daga garin Filato.


Don mun lura cewa wannan alkali ba zai yi adalci ba, zai iya bada belin 'yan ta'addan. Saboda haka muna kira a dauke wannan shari'a zuwa Abuja kuma a canja mana Alkali. Saboda rashin hukunta masu laifi ne ya sa suke ci gaba da aikin ta'addanci a kasar nan. 

Idan har ana so irin wannan abun ya kare ya zama dole a hukunta su cikin gaggawa kuma ba mu yarda da beli ba. Domin 'yan ta'adda ne. Kuma ana bada belinsu za mu yi zanga-zanga a kasar nan.
Rariya.

No comments:

Post a Comment