Thursday, 15 November 2018

Chelsea: Hukumar Fifa za ta 'haramta' wa kungiyar sayen sabbin 'yan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana fuskantar hukuncin dakatarwa daga sayen sabbin 'yan wasa, bayan wani bincike da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta gudanar.


Ana zargin kungiyar ne da sayen wasu 'yan wasa wadanda ba su kai shekara 18 da haihuwa ba.

Wasu bayanai da aka samu daga shafin intanet na Football Leaks sun nuna cewa ana binciken kungiyar tsawon shekara uku a kan wasu 'yan wasa 19 da ta saya ciki har da Bertrand Traore.

Shafin ya ce 14 daga cikin 'yan wasan 19 ba su cika shekara 18 a duniya ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta Chelsea ta fitar ta ce " ta bai wa hukumar Fifa cikakken hadin kai".

Kungiyar ta ce "ta gabatar da kwararan hujjoji inda ta nuna yadda ta bi ka'idojin Fifa".
Kamar yadda shafin ya bayyana, bangaren ladaftarwa na hukumar Fifa ya umarci da a haramta wa Chelsea sayen 'yan wasa tsawon shekara biyu da kuma cin ta tarar fam dubu 45.

A watan Satumbar shekarar 2017 ne aka fara binciken kungiyar kan wannan batun.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment