Friday, 30 November 2018

Da sana'ar karen mota na fara>>Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa da sana'ar karen mota ya fara lokacin yana matashi bayan da yayi watsi da karatu a shekarar 1972, ya kara da cewa amma daga baya ya zama direba kuma baya jin kunyar fadin wannan labari a ko ina.


Gwamnan yayi wannan bayanine lokacin da kungiyar matuka keke Napep/ Adaidaita sahu suka kai mai ziyara inda suka tabbatar mishi da goyon bayansu a zabe me zuwa, jiya,Alhamis, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Ya ci gaba da cewa tunda har ya zama gwamna to suma su sani zasu iya zama duk abinda suke so a rayuwa saidai yace abu daya ne zai hana mutum yin nasara a rayuwa shine ya shiga wata harkar banza ko ta shaye-shaye, ya gargadi matukan da cewa su guji harkar shaye-shaye tana lalata rayuwa.

No comments:

Post a Comment