Friday, 9 November 2018

Da wuya idan dan wasan Arsenal, Danny Welbeck zai sake buga kwallo

Da alama sana'ar kwallon dan wasan Arsenal, Danny Welbeck ta zo karshe sakamakon raunin da ya ji a wasan da Arsenal din ta buga da Sporting CP jiya wanda aka tashi 0-0.


Wasu rahotanni dake fitowa sun bayyana cewa, raunin na Danny babbane duk da dai har zuwa lokacin yin wannan rubutu ba'a bayyana kalar ciwon ba a hukumance, saidai me horas da kungiyar, Unai Emery ya bayyana, bayan kammala wasan cewa, Danny na Asibiti, zasu jira su gani amma fa rahoton da suke samu na cewa ciwon babbane.

Wata majiya tace, ana tunanin fa shikenan dan wasan ba zai sake buga kwallo ba saboda raunin.

Koda dai zai sake buga kwallo to watakila ba a Arsenal ba dan kuwa dama a wannan kakar wasan kwantirakinshi da kungiyar zai kare to ga dukkan alamu kuma kamin ace ya warke daga wannan ciwon watakila an gama gasar.

No comments:

Post a Comment