Friday, 9 November 2018

‘Daidaita Albashi Ya Kamata A Yi Ba Kari Ba’

Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.


Kungiyar kwadago ta NLC ta nemi gwamnati ta kara wa ma’aikata albashi wanda hakan ya sanya suka shiga yajin aiki a watannin baya tare da yin barazana za su tsunduma cikin yajin aiki a ranar Litinin da ta gabata. 

Kungiyar kwadagon ta nuna rashin gamsuwa da matakin gwamnatin tarayya na gabatar da naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata inda suka bukaci a mayar da shi Naira dubu 30.

Kamata ya yi kungiyar kwadago ta NLC ta mayar da hankalinta wajen daidaita albashi a tsakanin ma’aikatun gwamnati ba wai kari ba, Alal mislai an fifita ma’aikatan da suke aiki a FIRS da CBN da NCC da NPA da NDIC da makamantansu fiye da kowani ma’aikaci, inda ma’aikatan wurin suka ninka sauran ma’aikatu albashi fiye da kashi 30 cikin 100. 

Bayan dukkanininsu aiki iri daya suke yi da sauran ma’aikatan. Shi ya sa za ka ga a irin wadannan ma’aikatu ba a kai dan talaka sai ‘ya’yan ‘yan siyasa ko sarakuna ko wasu manyan masu rige da mukaman gwamnati. Kuma ma kasuwannin da su suke zuwa iri daya ne da wadanda sauran ma’aikata ke zuwa amma an fifita su a kan saura. Irin wadannan ne abubuwan dubawa ba batun karin albashin da bai kai su muhimmanci ba. 

Mu koma baya kadan, a shekara 2016 ne dai aka kara kudin litar mai daga naira 86 zuwa 145 yayin da mafi karancin kudin da ake biyan ma’aikaci a Nieriya ya tsaya a kan naira 18,000 kamar yadda yake a da can. Karin kudin mai ya sa kayayyaki sun kara tsada a kasuwa, yayin da kudin shiga na ma’aikata shi kuma bai karu ba. Ko da an kara albashin za a kara shiga matsaloli fiye da yadda ake cikin a yanzu. 

Ina mai bai wa kungiyar kwadago na NLC ta koma ta sake tunanin abubuwan da za su amfani ma’aikata fiye da karin albashi. Ita kanta gwamnatin za ta sami gamsuwa daga wurin ma’aikatan ta yadda za su inganta ayyukansu ba tare da kyashi ba. Kungiyar kwadago ta yi kokari ta ga an gyara ababan more rayu kamar su wutan lantarki, kyakkyawan ruwan sha, hanyoyi, inganta harkar lafiya da habaka tattalin arziki. 

Wadanan abubuwa su suka fi mahimmanci fiye da karin albashi, domin idan aka samar da ababan more rayuwa kowani ma’aikaci zai more albashinsa cikin kwanciyar hankali da wadata komi kankancinsu kuwa.

Daga Usman Hamisu, Kaduna.

08160874213

LEADERSHIP A YAU 

No comments:

Post a Comment