Friday, 30 November 2018

Dan Arewa ya samu sakamakon Digiri me kyau da aka kwashe shekaru 33 ba'a taba samun me irinshi ba

Bayan Kwashe Shekaru 33 Baa Taba Samun Sakamakon A Mataki Na Daya (First Class Honor B A History)  A Arewacin Nijeriya


Umar Aminu Yandaki, dan asalin jihar Katsina, wanda ya kammala digirinsa a bangaren tarihi a Jam'iar Usmanu Danfodio Sokoto a wannan shekara. 

Idan dai za a iya tunawa Farfesa Muhamud Yakub, Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa ne na farko a kaf din arewacin Nijeriya shekaru talatin da uku da suka wuce, da ya taba samun irin wannan sakamakon, tun daga nan ba a kara samu ba sai bana.
Rariya.

No comments:

Post a Comment