Friday, 2 November 2018

Dan Obasanjo ya kaiwa shugaba Buhari ziyara

Dan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, Olujonwon kenan a lokacin da ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a daren jiya a fadarshi ta Villa, sun yi ganawar sirri.Bayan fitowarshi ya shaidawa manema labarai cewa yana goyon bayan shugaba Buhari saboda irin ayyukan ci gaba da yake yi a kasarnan kuma wannan ne karin farko da aka samu gwamnati da ta damu da talakawa.

Ya kara da cewa yana girmama mahaifinshi amma wannan ba zai hanashi fadin gaskiya ba


No comments:

Post a Comment