Thursday, 8 November 2018

Didier Drogba zai yi ritaya daga buga tamaula

A ranar Alhamis ne dan wasan dan Ivory Coast kuma dan Chelsea Dideir Drogba ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa.


Dan wasan zai iya cimma gagarumar nasara idan kulob dinsa ya lashe wata gasa a Amurka.

Dan kwallon mai shekara 40, yana buga wa kulob din Phoenix Rising ne a Amurka, kungiyar da ya jagoranta har ta kai wasan karshe a gasar.

Kungiyar na fatan buga babbar gasar ajin kwararru ta Amurka.

Drogba wanda yana daya daga cikin 'yan wasan da suka ci wa kungiyar Chelsea kwallaye a raga, sau biyu yana lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka - wato a shekarar 2006 da kuma 2009.

Sau biyu yana lashe kofin gasar firimiya da kofin Gasar Zakarun Turai sau daya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment