Thursday, 8 November 2018

Diyar Atiku Abubakar za ta gurfana gaban majalisa saboda rashin biyan ma'aikata Albashi

Diyar Atiku Abubakar, Fatima Atiku Abubakar wanda kwamishiniyar kiwon lafiya ce a jahar Adamawa za ta gurfana a gaban majalisar dokokin jahar Adamawa don amsa tambayoyi game da matsalar rashin biyan ma’aikata albashinsu.


Jaridar Sahara ta ruwaito majalisar gayyaci Fatima da ta gurfana a gabanta ne a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba domin ta basu gamsashshen bayanai game da rashin samun albashi na tsawon watanni shida da wasu ma’aikatan ma’aikar kiwon lafiya basu yi ba.

Haka zalika majalisar ta aika ma wasu manyna jami’a daga ma’aikatar ta kiwon lafiya da su gurfana a gabanta, bugu da kari ta gayyaci babban akantan jahar Adamawa Augustine Wandamiya akan shima ya kawo kansa majalisar don basu bayani game matsalar albashin.

Kaakakin majalisar dokokin jahar Adamawa, Kabiru Mijinyawa ne ya bayyana haka a yayin da ya jagoranci zaman majalisar na ranar Laraba, inda yace makasudin gayyatan jami’an gwamnatin shine game da matsalar albashin wasu sabbin ma’aikata da ma’aikatan ta dauka aiki.

“Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi a karkashin shugabancin Hassan Barguma, shugaban masu rinjaye a majalisar, don ta bincike yadda gwamnatin jahar ta kashe naira biliyan biyu da babban bankin Najeriya, CBN, ya bata a matsayin bashi don aikin noma.” Inji shi.

Bayanai sun tabbatar da cewa CBN ta baiwa jahar Adamawa bashin naira biliyan 2 ta hannun kamfanin habbaka hakar noma da zuba jari dake jahar Adamawa AADIL, don a rabasu ga manoma.

Don haka a lokacin da shugaban kamfanin John Garba da manajan kamfanin Ibrahim Dasin suka bayyana gaban majalisar, sai majalisar ta umarcesu dasu gurfana gaban kwamitin da ta kafa.
Legit.ng

No comments:

Post a Comment