Wednesday, 7 November 2018

Duk wanda be taba aikata laifin da ya fi na dafa kafadar mace ba ya fito ya gayamin>>General BMB

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya sake fitowa inda ya mayar da martani ga masu sukarshi akan hoton da ya dafa kafadar abokiyar aikinshi, Rahama Sadau.


Hoton da Bello ya saka a shafinshi na sada zumunta ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka rika fadin be dace ba, Bello ya mayar da martani, saidai kuma ya sake mayar da wani martanin da wani salo na daban.

Bello yace yana kalubalantar masu sukarshi akan dafa kafadar Rahama Sadau da su fito su rantse cewa basu taba aikata laifin da yafi na dafa kafadar mace ba ko kuma ma basu taba aikata zunubi ba.

Saidai mafi yawa da suka bayyana ra'ayi akan wannan magana ta Bello sun bashi shawarar cewa ya bar maganar ta wuce kawai in ba haka ba ranshine zai ta baci a banza, a cikin su hadda abokiyar aikinshi, Ummi Zeezee.


No comments:

Post a Comment