Friday, 30 November 2018

EFCC ta kama wani dan kasar Lebanon da makudan kudi

Wannan wani mutum ne dan kasar Lebanon da hukumar hana cin hanci ta kasa, EFCC ta kama me suna Abbas Lakis bisa zargin aikata ba daidai ba, hukumar ta samu bayanan sirri akan mutumin dake shirin ficewa daga Najeriya zuwa kasar ta Lebanon.


Ya taso daga Kano ne zuwa Abuja inda daga nan yake shirin wucewa zuwa kasarshi ta Lebanon da makudan kudin.

Yawan kudin da aka kamashi dasu sun haura dala miliyan 2 sannan akwai kudaden kasashen Saudiyya, China, Kasar hadaddiyar daular Larabawa da sauransu da aka kama mutumin dasu.No comments:

Post a Comment