Tuesday, 27 November 2018

Ganduje makiyi ne>>Kwankwaso

A karon farko tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi tsokaci kan bidiyon da ke zargin gwamna Ganduje da karbar cin hanci na dalolin Amurka.


A cewar sa, "Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi. saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri."

Sanata Kwankwaso ya ce dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda abin da ake zargin gwamnan jihar da aikatawa.

Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya rikida ya koma makiyi.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin yin aiki tukuru wajen ganin an sauya "wannan gwamnati rubabbiya."

Ya ce ayyukan da dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Alhaji Abba Kabir ya yi a lokuta daban-daban za su ba shi damar yin nasara a zaben 2019.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment