Friday, 30 November 2018

Gaskiyar lamari akan hotunan kamin biki na Maryam Booth da Sadik Zazzabi

Hotunan tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth da mawaki kuma jarumin, Sadik Zazzabi sun karade shafukan sada zumunta inda akaita tunanin ko zasu yi aurene?Dalilin da ya janwo wannan tunani kuwa shine yanayin da aka dauki hotunan dake nuna alamar soyayya a tsakaninsu sannan babu wani cikakken bayani da ya warware zare da abawa akan wadannan hotunan.

Ya zuwa yanzu dai wasu karin bayanai sun fito da suka warware dalilin yin wadannan hotuna.

Shafin Kannywoodexclusive ya bayyana cewa wadannan hotunan an daukesune dan yin wani sabon fim mai suna Gidan Biki kashi na 4 wanda MC Malam Ibrahim Sharukhan ke shiryawa.

Hakan ta kara fitowa fili bayan da shima MC Sharukhan ya wallafa hotunan a shafinshi inda yayi musu lakabi da, Allah ya kaimu Gidan Biki.


No comments:

Post a Comment