Friday, 2 November 2018

Gwamnan jihar Kaduna ya dauki mace, Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarshi

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kenan tare da matar da ya dauka, Dr. Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarshi da zasu yi takara tare a zaben shekarar 2019 me zuwa.


Gwamnan ya bayyana cewa ya dauki shawarar zabar Dr. Hadiza Balarabene saboda karfafawa mata gwiwa da ya saka a gaba kuma hakan na zuwane sakamakon mataimakin gwamnan na yanzu, Barnabas Bala Bantex zai tsaya takarar sanatan Kaduna ta kudu.

No comments:

Post a Comment