Friday, 9 November 2018

Gwamnati Ta Kasa Biyan 30,000 Ga Ma'ikata A Wata Amma Duk Wata Zakzaky Yana Cin Abincin Naira Miliyan 3.5


Gaskiya wannan maganar da Ministan yada labarai ya fada Mista Lai Muhammed na cewa duk wata suna ciyar da Zakzaky Abinci Naira Miliyan 3.5 gaskiya inaga wannan rainin hankali ne da kuma rashin adalci ga sauran mutanen Nijeriya.Ana ta fama da Ma'aikata suna ta Kokarin tafiya yajin aiki akan sunaso abiyasu Naira Dubu 30 kacal amma Gwamnatin tace bata da kudi wai kuma sai gashi Gwamantin tana cewa tana ciyar da Zakzaky Abinci kusan Miliyan 3 kaga kenan Kullum kusan Naira Dubu Dari da goma sha biyar yake ci (115,000).

Gaskiyar magana kawai inde da gaske ana kashe wadanan kudin to wallahi ana mana asarar dukiyar kasa, ya kamata kawai Gwamnatin ta sake shi abar kashe wannan kudin. Idan kuma karya ne to kawai mu abar fada mana kar kusa hawan jinin mu ya tashi, Ehen.

Ai ko Kullum saniya ake dafa masa be kamata yaci wannan kudin ba, abar kashe kudin azo Atemakawa mutane marassa karfi. Dan Allah yanzu idan akayi lissafi daga kamashi zuwa yau kusan Shekara 3 nawa kenan?
Ra'ayin Sa'adatu Umar.

No comments:

Post a Comment