Tuesday, 6 November 2018

Gwamnatin India ta hana sallah a babban masallacin Taj Mahal na kasar

Hukumar Bincike Kan Kayan Tarihi ta Indiya ta hana a yi Sallah a Masallacin Taj Mahal mai dimbin tarihi. 


Jaridar Times of India ta bayar da labarin cewa, Kotun kolin Indiya bayan ta bayar da hukuncin hana Sallar Juma'a a Taj Mahal a watan Yulin bana, a yanzu kuma ta hana Sallolin Khamsu Salawat a cikinsa.

Jami'an Hukumar sun janye motar da ake kai ruwa don yi alwala a Masallacin inda Limamin Masallacin Sadik Ali ya bayyana ya yi mamakin daukar wannan mataki da aka yi.

Shugaban Kula da Masallacin Sait Ibrahim Hussain ya ce, a tsawon shekaru ana Sallah a Taj Mahal kuma babu wani dalili da zai sanya a hana hakan a yanzu inda sun dauki matakin kai orafi ga Hukumar da ta yi hakan.

Hussain ya kara da cewa, sun ga alamun gwamnatin kasar ko ta yankin na da nuna kyama ga Musulmai.

Gwamnatin kula da Agra ta ce, a yanzu jama'ar yankin ne kadai za su yi Sallah a wajen inda aka hana masu zuwa daga cikin gari.

Tun bayan yanke hukuncin watan Yuli aka hana Muslmai Sallar Juma'a a Taj mahal sai wadanda suke zaune a yankin Agra.

A shekarar 1632 Turkawa suka gina Taj Mahal a Agra wanda yana daya daga cikin muhimman wurare masu ban mamaki guda 7 na duniya.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment