Tuesday, 6 November 2018

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.036 Don Gyara Hanyoyi

Zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da gaggauta gyaran hanyoyi 31 dake cikin kwaryar birni Kano wanda aka tsara aiwatar da aikin cikin kaso kaso wanda aikin zai lakume Naira Biliyan 1,036,389,164.33.

Jawabin haka ya fito daga bakin Kwamishinan ma’aiaktar yada Labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba cikin bayanin bayan taron majalisar zartarwar jihar Kano, Yace Ma’aikatar kudi ta Jihar Kano tuni ta bada umarni fitar da kaso 30% na adadin kudaden ga ‘yan Kwangila takwas domin fara aikin cikin gaggawa.

Kwamishinan yada Labaran ya ci gaba da cewa rashin kyawun hanyoyin na kawo cikas ga ci gaban da ake ganin na Jihar Kano a matsayin wani kasaitaccen birni mai dadadden tarihi, wanda kuma yin wanann gyara shi ne Gwamnatin Kano tafi mayar da hankali akansa.

Wasu daga cikin hanyoyin da ake sa ran fara aikin gyaransu sun hada da titin asibitin Nasarawa, Sheikh Jafar,titin da ya zagaya Kano, Unguwa uku, Bomfai, Abbatour, Cibic Center, Titin Obasanjo, Bello Road, Manladan, titn Kul-Kul, titin ‘yantsaki, Tudun Murtala, Sharada, Rijiyar Zaki, Kafin Dan Nana, Ashtom road, Titin fadar mai martaba Sarkin Kano, Kofar Fanfo, ‘Yan Katako – Zariya Road da sauransu.

Sauran abubuwan da zaman Majalisar ya amince dasu sun hada da sanya na’urar kara hasken wutar Lantarki guda 100 masu karfin doki daban daban, wanda za’a rabawa garuruwa daban daban wanda suka kama kudi Naira Miliyon of N574, 363, 062.00.

Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa an kuma amince da kashe Naira N31, 853, 503.5 domin ciyar da makarantun kwana na daiban firamare wanda suka hada Firamaren kwana ta Shehu Minjibir, firamaren kimiya ta Musa Saleh Kwankwaso da kuma Makarantar masu bukata ta musamman dake Mariri.

Hakazalika Kwamishina Malam Muhammad Garba ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba Gwamnatin Kano zata zagaye daukacin makarantun da basu da shinge, sanann kuma gwamnati ta haramta gina shaguna ajikin katangun makarantun firamare da Sakandire da asibitoci da kuma kotuna, kamar yadda Kwamishinan yada Labaran ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau.

No comments:

Post a Comment