Friday, 16 November 2018

Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi

Gwamnatin tarayya ta hannun ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ta bayyana ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu dan yin Maulidin annabin tsira, Muhammad (S.A.W).


Ministan yayi kira ga musulmai da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammad(S.A.W) da suka hada da kyauta, hakuri da juna, zaman lafiya da sauransu.

No comments:

Post a Comment