Saturday, 17 November 2018

Hadiza Bala Usman ta karyata Sahara Reporters, tayi barazanar zuwa kotu

Shugabar hukumar kula da tashoshin ruwa, NPA, Hadiza Bala Usman ta fito ta karyata labarin da shafin Sahara Reprters suka buga na cewa tana da hannu a murdiyar zabe da bayar da rashawa.


A sakon data fitar ta dandalinta na sada zumunta, Hadiza ta bayyana cewa, hankalinta ya kawo kan labarin na Sahara Reporters wanda yace ta bayar da kudi dala miliyan 2 dan a baiwa Uba Sani tikitin jam'iyyar APC na takarar sanatan Kaduna ta tsakiya.

Hadiza ta kara da cewa, Shafin Sahara Reporters da suke ikirarin girmama 'yancin dan adam ya kamata ace suna tantance gaskiyar labari kamin su buga shi.

Dan haka tana bukatar a cire wannan labari da suka buga a kanta nan da sati daya ko kuma su kawo hujja akan labarin ko kuma taje kotu.

No comments:

Post a Comment