Friday, 9 November 2018

Har yanzu shekarau ne dan takarar mu>>APC

Shugaban jam'iyar APC na Kano Alh Abdullahi Abbas ya bayyana labarin da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa an karbe takarar Malam Ibrahim Shekarau daga kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a bisa zargin sa da almundahana ba gaskiya bane. Labari ne mara tushe.


Alh Abdullahi Abbas  ya bayyana hakan ne a jiya yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano.

A karshe ya yi kira da jama'a da su yi watsi da wanan labarin wanda yace ba shi da tushe bare makama. Ya ce Malam Shekarau  ne dan takarar da jam'iyyar APC ta sani.
Rariya.

No comments:

Post a Comment