Wednesday, 7 November 2018

Hotuna daga yanda Shugaba Buhari ya amshi rahoton karin albashin ma'aikata: Ya sha alwashin aikashi majalisa nan bada dadewaba

A jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi kammalallen rahoto daga kwamitin da suka yi aikin duba karin albashin ma'aikata zuwa dubi 30.A lokacin da yake amsar rahoton, shugaba Buhari ya sha alwashin yin aiki tukuru dan ganin wannan rahoto ya zama doka inda yace nan ba da dadewa ba zai aika dashi ga majalisa dan su yi muhawara su kuma tabbatar dashi a matsayin doka.

Shugaban yayi kira ga ma'aikata da kada su zama 'yan koron 'yan siyasa da za'a rika amfani dasu wajan cimma wata manufa ta daban

No comments:

Post a Comment