Thursday, 29 November 2018

Hotunan kamin biki na Maryam Booth da Sadik Zazzabi

Wadannan hotunan na tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth da tauraron mawaki kuma jarumi, Sadik Zazzabi da suka dauka dake nuna alamar soyayya tsakaninsu sun cika shafukan sada zumunta kuma sun dauki hankula sosai.Shin aure zasu yi?
Tambayar da kusan da yawa daga cikin wadanda suka ga wadannan hotunan suka fara yi kenan saidai babu gamsashshiyar amsa.

Da farko dai an ga hotunan a shafin shahararren me daukar hotonnan, Balancy inda ya saka yayi kalaman soyayya sannan ya musu murnar aure. Har ya kira Maryam din da sunan Amarya.

Daga nan kuma sai a shafin shahararren me kwalliyarnan, Mansurmakeup, inda yace wadannan hotunan kamin bikine na Maryam din da sadik amma kada ace a bakinshi aka ji.

Daga nan kuma sai ita Maryam din da kanta ta saka a shafinta na dandalin Instagram inda tace ga labari ku yadashi kamar biskit din iyali, ta yi kari da saka ranar 3/12/2019.

Shidai sadik be saka komai ba shafinshi na dandalin Instagram zuwa lokacin yin wannan rubutu.

Koma dai menene sai muce lokaci be bar komai ba kuma muna musu fatan Alheri.No comments:

Post a Comment