Thursday, 15 November 2018

Hukumar DSS Ta Nemi Buhari Ya Hukunta Oshiomhole Kan Cin Hanci


Hukumar tsaro ta farin kaya ( DSS ) ta rubutawa Shugaba Muhammad Buhari kan ya hukunta Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole bisa zargin karbar cin hanci har ta Dala milyan 55 daga hannun 'yan takara na zaben fidda gwani.

A cikin rahoton da DSS ta aikawa Buhari da kuma Hukumar EFCC, ta nuna cewa Gwamnan Zamfara ya bayar da cin hannun Dala milyan 17 sai dan takarar Gwamnan na jihar Imo wanda ya bayar da Dala milyan uku. Hukumar DSS ta nuna cewa a cikin asusun a jihar bankin wata 'yar uwarsa ce a rika saka kudaden cin hancin.

No comments:

Post a Comment