Monday, 5 November 2018

Ina da Alwala lokacin dana dafa Rahama Sadau kuma ba shafata na yi ba>>General BMB

A jiyane muka ga hoton taurarin fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB da Rahama Sadau inda Bellon ya dafa kafadarta, hoton ya dauki hankula ya kuma jawo cece-kuce sosai inda wase suka ta sukar yanda Bellon ya dora hannu a kan Rahamar, tun a jiyan Bello ya ta mayar da martani amma ya sake mayar da martani na musamman.


A wani bidiyo da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Bello ya kare dafawar da yawa Rahama Sadau inda yace' yana da dangantaka ta jini da kowace musulma, sannan kuma yana da dangantaka ta mutuntaka da duk wani dan Adam, dan haka Rahama Sadau 'yar uwarshi ce ta jini kuma dan na dafata mun dauki hoto, ba shafata na yi ba, kai kamin ma in dafata inada alwala a jikina kuma abinda ke karya alwala sune, maniyi, maziyi, bawali gahidi, suma maye, shafar mace, shafar alkalami, bacci, ridda, saboda haka dan Allah dan Annabi hadisai kuke kawo min kuma nima hadisi na kawo muku dan Allah dan Annabi ku yi hakuri kowa ya rike ra'ayinshi, Allah, ubangiji shi kadai yasan karatun bebe kuma Allah shi kadai yasan daidai, Allah ne mafi sani, nagode Allah ya muku albarka' 

No comments:

Post a Comment