Tuesday, 27 November 2018

Ina Goyon Bayan 'Yan APC Da Suka Maka Jam'iyyar Kotu Kan Zaben Fidda Gwani>>Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya fito fili ya goyi bayan 'yan takarar APC na zaben fidda gwani wadanda suka maka Jam'iyyar kotu bisa rashin adalcin da aka yi masu a lokacin zabukan.

Tun da farko dai, Shugabannin Jam'iyyar APC na kasa sun yi barazanar ladaftar da duk wani dan takarar Jam'iyyar wanda ya shigar da kara bayan da jam'iyyar ta baiwa wasu 'yan majalisa tikitin tazarce duk da yake ba su ci zaben fidda gwanin ba.
Rariya.

No comments:

Post a Comment