Thursday, 8 November 2018

Jam’iyyar APC Ta Karyata Rahoton Da Ke Cewa DSS Ta Kama Oshiomhole

Jam’iyyar APC ta karyata cewa, jami’an hukumar DSS sun cafke shugaban jam’iyyar, Kwamrade Adams Oshiomhole, kamar yadda ake rade radi a kafafen watsa labarai na kasar nan.


LEADERSHIP A Yau ta ruwaito cewa, jami’an rundunar DSS sun cafke shugaban jam’iyyar APC din ne ranar Lahadi daddare sakamakon korafin da gwamnonin jam’iyyar suka yi na cewa, ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben fidda gwani da aka gudanar kwanannan.

Da yake mayar da martani a kan zargin cewa, shugaban jam’iyyar ya fuskanci tambayoyi daga jami’an DSS, Jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa, a halin yanzu Mista Oshiomhole ya yi tafiya zuwa kasashen waje, a saboda haka ba shi da lokacin da zai bata na mayar da martani a kan wannan rade radin.

Ya kuma kara da cewa, shugaban jam’iyyar, Kwamrade Oshiomhole, ya tafi kasashn waje ne ranar Litinin don gudanar da harkokin kashin kansa, ya kuma ki yin karin bayani a kan a bin dake tattare da tafitar nasa.

Ya kuma kara da cewa, “Bamu da wani karin bayani a kan wannnan rade radin, shugaban jami’iyyar bas hi a cikin kasar balle ya gaskata ko kuma ya katyata labarin.

A bayanin ya nuna cewa,wai, jami’an DSS din sun bukaci ya yi murabus daga bakin aikin nasa ne saboda korafe korafen day a biyo bayan yadda ya gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar kwanan nan.

No comments:

Post a Comment