Thursday, 8 November 2018

Kalli abinda Mourinho yawa magoya bayan Juve da ya kusa sa su dambace da dan wasan kungiyar

Bayan kammala wasan Man U Da Juventus jiya, me horas da 'yan wasan na Man U, Jose Mourinho wanda mutum ne da yayi suna wajan kuri da cika baki, yayi wani abu da ya jawo cece-kuce da kuma har wani dan wasan Juven ya tunkareshi cikin fushi.


Bayan kammala wasan da aka tashi Man U na cin Juve 2-1, Mourinho ya shiga fili inda ya sa hannu ya karkato da fatar kunnenshi ta baya sannan ya karkata baki, irin alamar yana so ya ji ci gaban ihun da masoyan Juventus ke yi, wannan abu ya jawo hargowa wanda har saida dan wasan Juve, Leonardo Bonucci yayi kan Mourinho cikin fushi, sai da dai ma'aikatan UEFA suka fitar da Mourinhon daga tsakiyar fili.

Dama ko da a wasan da suka buga a gidan Man U wanda Juve din ta ci 1-0, bayan kammala wasan saida Mourinho ya dagawa masoyan Juve dake sowa yatsu 3, watau yana nuna musu kofunan da yaci a yayin da ya horas da babbar abokiyar hamayyar Juve din, Inter Milan, Champions League, Serie A da Italian Cup a kakar wasa ta 2009/10.

Da yake magana da manema labarai bayan wasan, Mourinho ya kare abinda yayi inda yace, yazo ne yayi aikinshi anan amma an yi ta zaginshi da iyalanshi, shi yasa yayi hakan yaji yaya ina ihun nasu ya tafi? Mourinho yace be kamata yayi hakan ba kuma bazai sake yi ba amma baya tunanin ya bakantawa kowa rai kuma hakan da yayi amsace wadda ta dace ga wadanda suka zagi iyalinshi.

No comments:

Post a Comment