Thursday, 1 November 2018

Kalli yanda jama'ar gari suka jera layi dan taya dakin karatu kwashe kaya: Gwanin birgewa

Wadannan hotunane daga birnin Southampton na kasar Ingila inda jama'ar garin suka taru suka taya wani dakin karatu komawa mazaunin dindindin bayan da aka mishi karin kudin haya a shagon da yake.Shagon litattafan me suna October Books ya saka sanarwa cewa yana neman taimakon yanda zai kwashe kayanshi daga tsohon shagon da zai bari zuwa wanda ya siya da kudin taimako da na bashi.

Ranar da zai tashi din kuwa sai ga mutane sama da 250 sun zo dan tayashi kwasar kayan, kamar yanda Buzzfeed ta ruwaito.

Mutanen sun jera layi daga tsohon shagon litattafan zuwa sabon shagon inda suka rika mika-mika har aka kwashe kayan shagon kaf.

Yanayin abin ya dauki hankula.
No comments:

Post a Comment