Wednesday, 7 November 2018

Karanta bukatun ban mamaki da Mbappe ya jewa PSG da su lokacin da zasu sayeshi

Wasu bayanan sirri sun fito da Der Spiegel ta wallafa yau, Laraba akan bukatun da dan wasan kasar Faransa, Kylian Mbappe ya je wa PSG dasu a lokacin da zata sayeshi daga kungiyar Monaco a shekarar 2017 lokacin yana da shekaru 18.


Bukatun sun baiwa mutane mamaki.

Wasu daga ciki sune, iyalan Mbappe sun bukaci PSG ta biyasu diyya idan sanadiyyar sayen Mbappe hukumar wasannin turai ta UEFA ta hukuntata ta hanata zuwa gasar cin kofin zakarun turai da kuma idan dan wasan ya ci kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d'Or PSG din zata mayar dashi wanda yafi karbar albashi me tsoka a kungiyar.

Saidai PSG bata amince da wadannan sharudda ba.

Haka kuma Mbappe ya bukaci a saka a cikin alkawari cewa za'a rika bashi awanni 50 duk shekara yana amfani da jirgin kungiyar, shima dai wannan bata amince ba, saidai maimakon haka ta bashi Yuro dubu 30 dan ya biya masu mishi aikin gida, direba da masu tsaron lafiyarshi.

Haka kuma mahaifin Mbappe ya bukaci a barshi ya rika halartar gurin atisayen kungiyar wanda shima PSG bata amince mishi ba.

No comments:

Post a Comment