Saturday, 17 November 2018

Karanta kaji dan kwallon da yafi kudi a Duniya, ba Ronaldo bane ko Messi

Daukaka da kudi wasu abubuwane mabanbanta da wasu kan samesu a lokaci guda wasu kuwa sukan samu daya yafi daya, idan ana maganar sana'o'in Duniya, kwallo na daya daga cikin wadda ake ganin cewa tana gaba-gaba wajan kawo kudi masu tsoka to saidai ko wane dan wasane yafi kudi a Duniya?.


Cristiano Ronaldo da Messi 'yan wasane da a wannan zamanin suke taka leda na tsawon lokaci da ba'a taba gani ba kuma hakan ya sa sunayensu sun daukaka sosai a Duniyar kwallo.

A yanzu idan dan kwallo ya shara, bawai ta Albashinshi kadaine zai rika samun kudi ba, akwai kamfanonin da zasu iya bashi talla su kuma rika biyanshi makudan kudi wanda suka fi ma albashin da kungiyar kwallonshi ke biyanshi.

Saboda yawan mabiya da yake da su a shafukan sada zumunta, Ronaldo nawa manyan kamfanonin Duniya irin su NIKE, EA Sport, dadai sauransu talla, kuma shine dan kwallon da yafi ko wane dan kwallon kafa samun kudi ta hanyar yiwa kamfanoni talla inda ya samu dala miliyan 450.

Me biye mishi shine Messi wanda shi kuma ya samu dala miliyan 400 daga yiwa kamfanoni talla kamar yanda Goal ta ruwaito.

Saidai idan aka koma yawan albashin da kungoyin kwallon kafa ke biyan 'yan wasa, Messi na gaba da Ronaldo inda yake daukar dala miliyan 111 duk shekara kamar yanda Forbes ta ruwaito, mutane biyune kawai a harkar motsa jiki suka fi Messi Albashi, sune 'yan dambennan, Floyd Mayweather da Conor McGregor.

Akwai sauran 'yan kwallo da suke daukar kudade masu tsoka duk da basu kai ko rabin abin da Ronaldo da Messi ke dauka ba.

Misali Zlatan Ibrahimovic me daukar dala miliyan 190 sai Neymar dake daukar dala miliyan 185 sai Wayne Rooney dake daukar dala miliyan 160 sai kuma Gareth Bale dake daukar dala miliyan 125.

Akwai 'yan kwallon da duk da sun daina taka leda amma suna samun makudan kudi har yanzu, misali David Beckham dake daukar dala miliyan 450 sai kuma Ronaldo Nazario dake daukar dala miliyan 150.

Saidai duk wadanda aka lissafa a sama basu bane 'yan kwallon da suka fi kudi ba a Duniya.

Dan kwallon da ake tunanin shine yafi kowane kudi shine Faik Bolkiah dan wasan Leicester City me shekaru 20 da haihuwa wanda kuma dan uwane ga Sultan din Brunei, Hassanal Bolkiah wanda aka yi kiyasin yana da zunzurutun kudin da suka kai dala miliyan dubu 20.

No comments:

Post a Comment