Monday, 12 November 2018

Karanta labarin Kasar da babu masallaci ko daya

Kasa daya tilo a yankin nahiyar turai da ta rage wadda babu masallaci ko da ya itace kasar Slovakia, kasar bata amince da musulunci a matsayin addini ba kuma mutane 5000 kawai musulmai dake zaune a kasar suma kuma duk kusan turawane.

Ba'a yadda ayi aure irin na addinin musuluni ba ko kuma a nada wasu shugabannin addini ba a kasar kamar yanda TRT ta ruwaito.

An saka a dokar kasar cewa sai an samu sahannun musulmai 20,000 a kasar kamin a yadda da musulunci a matsayin addini a kasar wanda musulman kasar ba su da wannan yawan, a shekarar 2017 an nunka yawan wannan lamba fiye da sau daya.

Koda 'yan gudun hijirar dake ta kwarara yankin turai daga kasashen musulmai wannan kasa ta Slovakia ta ki karbar ko guda inda ta bayyana dalilin cewa bata da masallacin da zasu rika yin ibada.

'Yan siyasar kasar da dama sun bayya kiyayyarsu da addinin musulunci a fili.

No comments:

Post a Comment