Monday, 5 November 2018

Karanta matakin da wani yace zai dauka akan kaninshi in ya iskeshi suna wasan kanin miji da matarshi

Wasan kanin miji na daya daga cikin abubuwan al'ada da kusan duk da cewa ya ragu amma har yanzu akan dan taba sama-sama a wasu guraren, wani bawan Allah ya bayyana irin matakin da zai dauka akan kaninshi idanda zai sameshi yana wasan kanin miji da matarshi.


Bawan Allahn ya bayyana a dandalinshi na sada zumunta cewa, wasan kanin miji akwai dadi idan ana daka ya hau baya.

Ya kara da cewa, Bayan wa?(zaka hau) matar tawa? ashe dana sumar da kai.

Wannan magana tashi ta dauki hankula inda mutane suka bayyana ra'ayoyinsu akai.No comments:

Post a Comment