Monday, 5 November 2018

Kayar da Buhari zabe a 2019 abune me matukar wuya>>Cibiyar binciken kasar Amurka

Cibiyar Zaman Lafiya na Amurka (USIP) ta bayyana cewar zai yi matukar wahala a kayar da shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben 2019 da ke tafe.

Cibiyar ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar a kan babban zaben mai zuwa.

USIP ta ce an fitar da rahoton ne bayan tattaunawa da dimbin 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar.

Wannan rahoton na USIP ya ci karo da wasu hasashe guda biyu da Economist Intelligence Unit (EIU), ta fitar inda ta bayyana cewar akwai yiwuwar za a kayar da shugaba Buhari a shekarar 2019.
Rahoton ya ce "Yan Najeriya da dama suna ganin gwamnati ba ta cika alkawurran da ta dauka ba. Wasu kuma suna ganin cewar adadin mutanen da za suyi zabe a 2019 ba za su kai na 2015 ba saboda mutane lagwan mutane ya karye sai dai duk da hakan kayar da shugaban kasa abu ne mai wuya."

Idan aka kwantata zaben 2015 da na 2019 mai zuwa, rahoton ya bayyana cewa akwai yiwuwar barkewar rikici a jihohin Adamawa, Anambra, Ekiti, Kaduna, Kano, Legas, Plateau da Rivers idan aka kwatanta da sauran jihohin.

Rahoton ya ce ya zama dole hukumar zabe INEC da hukumomin tsaro su tashe tsaye domin ganin an kiyaye afkuwar rikicin ta hanyar gudanar da sahihin zabe makamancin wanda aka gudanar a 2015.
Legit.ng

No comments:

Post a Comment