Saturday, 10 November 2018

Kotu ta bada damar kama wadanda suka taimakawa Nnamdi Kanu

Babbar kotun Najeriya dake Abuja ta amince da bukatar da aka shigar gabanta, ta neman baiwa jami’an tsaron Najeriya damar kama wasu mutane dake zargin sun taimakawa Nnamdi Kanu jagoran kungiyar IPOB, mai neman kafa kasar Biafra tserewa daga kasar.


Mutanen da ake zargi da aikata laifin sun hada da tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Femi Fani Kayode, Sanata Eyinayya Abaribe, Tochukwu Uchendu da kuma wani Emmanuel Shallom Ben, wadanda sunayensu ke kunshe cikin takardar karar da Isiah Ayugu ya gabatarwa kotun.

Isiah Ayugu wanda ya gabatar da kansa a matsayin lauya, kuma dan Najeriya mai kishin kasa, ya kuma nemi jami’an tsaro su kama lauyan Nnamdi Kanu Ifeanyi Ejiofor da kuma wasu ‘yan uwan jagoran na IPOB Emmanuel Kanu da Uchechi Kanu.

A cewar Ayugu, wadanda yake zargin sun taka rawa wajen yada labaran karya kan cewar sojojin Najeriya sun kama Nnamdi Kanu, tare da azabtar da shi, daga bisani kuma suka hallaka shi, a lokacin da jagoran kungiyar ta IPOB da aka haramta ya bace.

Yayin da yake sanar da hukuncin amincewa da umarnin da kuma shigar da karar, mai shari’a John Tsoho ya tsayarda ranar 22 ga watan Nuwamba domin soma sauraron shari’ar.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment